Darasin Fizis Da Hausa Kashi Na Daya

Spread the love

RUBUTU NA FARKO A JADAWALIN KOYON PHYSICS DA HAUSA

PHYSICS 001

MA’ANAR PHYSICS;

Physics ada ana kiransa da Natural philosophy, ya shafi al’amura da yawa akan duk halittun da suke duniya (Nature) kamar su, (Tsirrai da dabbobi da ruwa da iska da duwarwatsu da sauransu) wadda ake fahimtarsu ta hanyoyi masu sauki karkashin hikima da ilimi mai zurfi.

Bayan lokuta sunyi nisa, an samu kwararrun masu ilimin kimiyya daban-daban da suka fito daga Physics kuma suka dogara da kansu a fage na bincike.

Ta wannan hanyoyi, Physics ya kara rike manufofinsa wajen fahimtar yadda zubin halittun duniya suke (Structure of the natural world) kamar su (Duwarwa, tsirrai da dabbobi da sauransu)
sannan yayi cikakken bayani akan Natural phenomena kamar(Gravity da saurasu).

Manyan rabe-rabe na Physics sune Mechanics da kuma Field theory.

Mechanics ya shafi ilimin motsin kananan abubuwa ko manyan abubuwa karkashin aikin maganadisu (Force) wanda shine yake sa abubuwan su motsa.

Physics na Field kuwa ya shafi ilimin sanin asali da yanayi da dabi’un Gravitational, electromagnetic, Nuclear da kuma sauran force Fields.

Idan ka hada, Mechanics da Feild theory sun zama sune mahimman abubuwa wajen fahimtar Halittun duniya wanda ake ganinsu da wanda ba aganinsu sai dai kaji su ko ka taba su (Natural phenomena) wanda kimiya ta samar.

Daga nan zamu iya cewa, Physics na nufin ilimin kimiya na zahiri (Physical sciences) dake taimakawa wajen gane dabi’un komai na duniya(Matter) da yadda suke da alaka da makamashi (Energy).

Sannan kuma zamu iya cewa Physics zai iya zama kimiyyar gwaje-gwaje (Science of measurement).

A takaice Matter na nufin komai na duniya mai rai ko mara rai (Matter is anything that has mass and occupy space), tunda komai na duniya nada nauyi kuma yaci guri to dan haka komai na duniya Matter ne, Misali abun da yafi ko wanna abu rashin nauyi a duniya (Most lighter element) itace iskar Hydrogen kuma itama Matter ce.

Nayi sharshin ma’anar Matter ne kawai ba bayani ba duba da kalmar ta futo acikin rubutun mu asama.

Yawan karatu da bibiya shike sa a zama daga cikin masana.

Tsarawa Da Gabatarwa kungiyar
Arewa Student’s Orientation Forum (ASOF)
(08038485677)

Mu hadu a rubutu nagaba

️Abba Haladu Umar
08034343929

Leave a Reply