Sakakin likitoci Me shirin tafiya bautar kasa ya rasa kafarsa

Spread the love

Daga. Nazir Muhammad.

Sen. Mahmud Auwal yarone da ya kammala karatunsa a bangaren kimiyyar siyasa a jami’ar Bayaro Wanda har mukamin Senator mai wakiltar sashensu ya yi, yanzu haka yana jiran tafiya bautar kasa kenan, ya gamu da barayi ne akan hanyarsa ta zuwa banki a garin port Harcourt inda suka harbe shi a kafa a take aka rankaya da shi asibin koyarwa na jami’ar port Harcourt inda aka kashe kudi sama da Naira miliyan daya domin ceto rayuwarsa a inda likitocin asibitin bangaren kashi suka yi sakaci har kafarsa ta rube ta fara wari, Shawara ta canza daga bisani Aka dauke shi zuwa Asibitin Malan Aminu Kano a inda likitoci suka tabbatar da ribewar kafarsa Wanda hakan ya jawo dole aka yanketa ba tare da bata lokaci ba, a yanzu da kungiyar matasan arewa mazauna kudancin Nigeria na yunkurin tsayawa domin karbar masa hakkinsa bisa sakaci da likitocin Assibitin koyarwa na Port Harcourt suka yi akan ruguza masa mafarkinsa,
Abin tausayi shi ne taya yanzu Abbati zai fara Sabin rayuwa ba tare da kafa ba?
Mafarkin Abbati ya zama shudadde domin burinsa bazai samu cikuwa ba lallai ya kamata sauran kungiyoyin hakkin dan Adam su musamman Yan arewa su zo guri daya domin nema masa hakkinsa Allah ya ba shi lafiya Albarkan Annabi s.a.w

Leave a Reply