Anya Ko Zai Sake Cin Zabe?Wani Dan Majalisa Ya Ci Mutuncin Al’ummar Da Yake Wakilta.

Spread the love

Kamar Yadda Jaridar Katsina Daily Post ta Rawaito, An nadi faifan muryar Dan majalisar mazabar Mashi da Dutsi Hon. Mansur Ali Mashi inda aka ji;-

Yana caccakar yan mazabarsa da yake wakilta na Mashi da Dutsi ya kirasu da kauyawa marasa Wayo.

A faifan muryar da aka ji mai maganar na alakanta kansa da mazaba da yake wakilta ta Mashi da Dusti, an jiyo yana cewa shugaban kasa Buhari ya gaza Cikawa Yan Nigeria Al’kawuran su.

Sannan kuma ya ce a mazabarsa, ya taba biya ma wani aikin hajji amma da mutumin ya dawo sai ya ce yanzun aure yake so ya yi masa.

A maganar da aka nada an ji inda yake cewa ko da dan majalissar Malumfashi da Kafur Hon. Talau ya koma majalissar Wakilai sau uku sai da akai ta ta6a masa a zauren majalissar saboda yan Katsina ba su tura dan majalissa ya je ya wakimce su har sau uku.

Akwai maganganu da dama da aka gudanar a muryar da ake alakanta ta da cewa Hon. Mashi ne ya fade ta saboda irin yadda yake ambatar mazabarsa da kuma garinsa na Mashi bisa yadda yake cewa in ya je Mashi yadda mutane ke cika masa gida duk kuma kowa na zuwa ne don ya saurare shi

Kawo yanzun dai Hon. Mashi bai ce komai ba game da faifan muryar dake ta yawo a kafafen sadarwa, inda ake cewa shi ne ke wadannan kalaman.

Leave a Reply