Tsohon Firaministan Burtaniya David Cameron ya fadawa Buhari yadda zai magance ta’addanci a Najeriya ba tare da ya sauke Hafsoshin tsaro ba.

Spread the love

Babu abin da sauke manyan hafsoshin tsaron Najeriya zai kawo in ba kara dagula yaki da ta’addancin da sojojin Najeriya keyi ba, In ji Firaministan David Cameron.

Tsohon firaministan Burtaniya David Cameron ya ce ba sauke manyan Hafsoshin tsaron Najeriya ne zai kawo karshen ta’addancin da Najeriya ke fama dashi ba.

David Cameron ya ce babu abin da sauke manyan hafsoshin tsaron Najeriya zai kawo inba kara dagula yaki da ta’addancin da sojojin Najeriya keyi ba.

David Cameron yace babban abinda shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari yakamata yayi shine, zurfafa bincike a cikin ita kanta ma’aikatar tsaron ta Najeriya, da sauran hukumonin tsaron kasar.

David Cameron ya kara da cewa akwai Jami’an tsaron da ake hada baki dasu wajen fitar da bayanan sirri ga ‘yan ta’addan kasar, kuma su wadannan jami’an tsaron sun hada da sojoji da ‘yan sanda da kuma ‘yan sandan farin kaya.

David Cameron yace, sannan abu na biyu su Kansu al’ummar kasar ta Najeriya basa bawa jami’an tsaron kasar hadin kai wajen kawo musu bayanan sirri game da wani motsi da za suga wasu mutane nayi Wanda basu yadda dashi ba.

David Cameron yace dole sai su Kansu ‘yan kasar ta Najeriya sun hada kai da Jami’an tsaron ba tare da nuna tsoron ko wani Abu zai samesu ba in sukayi fallasa sannan gwamnatin kasar ta Najeriya zata fara shawo kan matsalar.

David Cameron yace don haka yana kira ga su Kansu yan kasar ta Najeriya dasu dakatar da kiraye kirayen a kori manyan hafsoshin tsaron ta Najeriya ba a nan matsalar take ba.

Leave a Reply