Da Dumi Dumi ance daliban da aka sace a jihar katsina mutun 200 sun dawo gida.

Spread the love

Dalibai dari biyu 200 da suka tsere domin tsira da rayukansu a daren Juma’a bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari makarantar sakandaren Kimiyya ta Gwamnati, dake ƙanƙara a Jihar Katsina, an dawo da su lami lafiya.

Kakakin rundunar ‘yan sanda, Gambo Isah da Shugaban makarantar, Usman Abubakar sun tabbatar da hakan ga manema labarai a wata sanarwa da suka raba wa manema labarai a yau ranar Asabar.

Wannan na zuwa ne yayin da rahotanni ke cewa an sace daruruwan mutane yayin samamen.
Kodayake har yanzu makarantar da jami’an ‘yan sanda ba su tabbatar da rahotannin sace ko asarar rayuka ba, Abubakar ya ce a yanzu haka jami’in gudanarwa da’ yan sanda suna kan binciken daliban.

“Da gaske ba za mu iya tantance yawan daliban da aka sace ba sai dai wasu daga cikin daliban sunka sake dawowa daga daji kusa da su. A yanzu haka muna karbar mahalarta. Wasu daga cikinsu kai tsaye sun tafi gidajensu daban-daban tare da iyayensu suna kiranmu cewa ’ya’yansu suna gida,” in ji Abubakar.

Da yake bayar da nasa bayanin, kakakin ‘yan sandan ya ce: “abin da ya faru shi ne jiya da misalin karfe 11:30 na dare, mun samu rahoton cewa’ yan fashi da makami dauke da bindiga kirar AK 47 sun kai hari a Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati.

A daidai Wannan Lokaci Gwamnatin jihar katsina da hadin gwiwar Rundunar Sojojin Nageriya da yan Banga sun kutsa daji domin neman daliban da aka sace…

Leave a Reply