Yan ta’addan Boko Haram sun kashe ‘yan Gudun Hijira mutun 27 a Garin Tumur.

Spread the love

Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe akalla mutane 27 a wani harin “dabbanci mara misaltuwa” a kudu maso gabashin Nijar a ranar Asabar.

Rahotan Daily trust ya bayar da rahoton cewa wasu mutanen sun jikkata yayin da wasu har yanzu ba a gansu ba a harin da aka kai da yammacin ranar Asabar a ƙauyen Toumour na yankin Diffa Wanda ‘yan Gudun Hijira daga Borno suke zaune a wajen
Shaidu da sauran jami’ai sun tabbatar da harin, wanda ya zo sa’o’i kafin zaben kananan hukumomi da na yanki da aka ci gaba a duk fadin kasar ranar Lahadi.

Wani jami’in yankin ya ce “Wasu daga cikin wadanda harin ya rutsa da su sun mutu ko kuma sun ji rauni ta hanyar harsasai, wasu sun kone a cikin gidajensu, wutar wani mummunan wuta da maharan suka kunna,”

Ya kara da cewa, tsakanin gidaje 800 zuwa 1,000, babbar kasuwar da motoci da yawa sun lalace.

Maharan kusan 70 sun isa Toumour da misalin karfe 1745 GMT a kafa, bayan sun zagaya tafkin Chadi, in ji jami’in. Harin da ya dauki awanni uku.

“Da farko sun far wa gidan basaraken, wanda kawai ya samu damar tserewa,” in ji shi.

“Hari ne na dabbanci mara misaltuwa,” in ji wani zababben jami’in yankin da ya nemi a sakaya sunansa. “Kusan kashi 60 na ƙauyen ya lalace.” (AFP)

Leave a Reply