Da Dumi Dumi Covid-19 El Rufa’i ya sake rufe Makarantun jihar kaduna

Spread the love

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da umurnin rufe duka manya da kananan makarantu na Gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar a matsayin wani mataki na dakile komowar cutar korona wacce adadin ta ke kara yawa a yan kwanakin nan a jihar da ma kasa baki daya.

A wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta jihar Kaduna ta fitar a yau Litinin ta ce kowace makaranta a jihar ta tabbatar ta rufe daga ranar Laraba 16 ga watan Disamba 2020

Sanarwar ta ce dokar ta shafi duka makarantu har da jami’o’i da manyan makarantu a fadin jihar Rahotan manuniya..

Leave a Reply