Hukumar, yaki da hana ta’ammali da miyagun kwayoyi ta Najeriya, NDLEA, ta ce ta fitar da sunayen wadanda suka samu nasarar a ci gaba da daukar ma’aikata da ta keyi,
Kakakin hukumar Jonah Achema, ne ya bayyana cikin wata sanarwa da ya aike wa kamfanin dillancin labarai na kasar nan a ranar Juma’a,
Mista Achema, ya shawarci wadanda suka nemi aikin da su ziyarci shafin hukumar na Intanet www, NDLEA gov-org domin ganin karin sunayen da aka wallafa bayan wadanda aka tuntuba ta sakon karta kwana da kuma Email,
A cewarsa mutane da dama sun nemi wannna aiki a kuma matakai daban-daban wasu ma har an kirasu domin su je a musu jarrabawa,
Wadanda aka tuntuba su, 5,000 za su je ma’aikatar CCNN da ke jihar Plateau domin tantance su tare da takardunsu, kuma za a fara ne tsakanin 10: ga watan janairun da muke ciki zuwa 23: ga watan za a rika fara, aiki a Kullum daga karfe 09:00: na safe
za a raba masu neman aikin zuwa kashi hudu domin aikin tantancewa, domin tabbatar da an bi dokar da kuma ka’idojin wannna annoba ta Covid-19: in ji mista Achema, Daga Abbakar Aleeyu Anache,