Kudin fansho: Yanzu haka Sojoji Mazan jiya da suka yi ritaya suna zanga-zanga a Abuja.

Spread the love

Sojoji da suka yi ritaya a yanzu haka suna zanga-zanga a Ma’aikatar Kudi ta Tarayya, Abuja, kan rashin biyansu basussukan fansho.

Tsoffin ma’aikatan suna rokon Gwamnatin Tarayya da ta amince da biyan bashin mafi karancin albashin da ke bin su tsakanin shekarar 2019 har zuwa yau.

Suna kuma neman a dakatar da duk wani cire kudi a kan fansho na dukkan jami’an kiwon lafiya da suka yi ritaya tare da sanya jami’an da suka yi yakin lokacin yakin basasa kan shirin fansho na soja.

Wani wakilin sojojin da suka yi ritaya, Anthony Agbas, wanda ya isar da wasika ga jami’ai a Ma’aikatar Kudi ya shaida wa gidan Talabijin na Channels cewa sun yi yaki domin kasarnan kuma sun cancanci a biya su fansho.

Ya kara da cewa suna fatan za a biya musu bukatunsu ba tare da wani bata lokaci ba, bayan zanga-zangar lumana.

Leave a Reply