Burtai ya Jinjinawa Sojoji Operation tura ta Kai bango a nasararsu kan Boko Haram.

Spread the love

Shugaban hafsin sojin kasa Tukur Buratai ya yabawa rundunar sojin sama ta Operation Lafiya Dole kan nasarar da ta samu na fatattakar ‘yan ta’addan Boko Haram a yankin Marte na Borno.

Daraktan, Hulda da Jama’a na Soja, Brig.-Gen. Sagir Musa, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa ranar Lahadi a Abuja.

Musa ya ce rundunar sojan sama ta taka muhimmiyar rawa wajen lalata manyan bindigogin ‘yan ta’adda bakwai a yayin yunkurin kai hari a kan sojojin da ke yankin a ranar Asabar.

Ya ce sojojin na Operation Tura Takaibango sun yi nasarar kwanton bauna kan ‘yan ta’addan a lokacin da suka yi yunkurin kai hari a wurin da sojojin suke a wajen garin Marte.

A cewarsa, Rundunar Sojan Sama ta taka rawar gani abin yabawa wajen lalata motocin bindigogi na ‘yan ta’adda bakwai da kuma lalata adadin wadanda ba a tabbatar da su ba na maharan.

“Babban hafsan hafsoshin sojan ya nuna matukar yabo da jinjinawa sojojin, musamman rundunar Sojin sama ta Operation Lafiya Dole saboda irin bajintar da suka nuna da kuma kishin kasa wanda ya haifar da nasarorin da aka samu.

“Ya bukace su da su ci gaba da karfafa gwiwa da kuma hanzarta aiki don tabbatar da saurin fatattakar ‘yan ta’addan Boko Haram / ISWAP a Najeriya,” in ji shi. (NAN)

Leave a Reply