Sanata Uba Sani da Gwamna El’rufa’i sun Jagoranci Tawagar Taron masu ruwa da tsaki na sabunta Rijistar Jam’iyar APC.

Spread the love

A wani Sako Mai dauke da hoto da Sanata Uba Sani ya wallafa a shafinsa na Twitter Yace A safiyar yau, na bi sahun Gwamna Nasir El-Rufai da sauran manyan masu ruwa da tsaki a wani taron masu ruwa da tsaki na shiyyar Kaduna ta Tsakiya (Zone 2) kan taron sabunta rajistar mambobin jam’iyyarmu ta All Progressive Congress (APC) a duk fadin kasar.

Taron ya kasance mai ban sha’awa, mai Kuma tasiri kuma an gudanar da shi cikin yanayi mai ma’ana. Masu ruwa da tsaki sun bayyana kudurinsu na tsunduma cikin wayar da kan membobin Jam’iyar don dorewar Nasara ga APC a jihar Kaduna. Sun himmatu wajen ganin sun sanya jam’iyar ta zama mai tasiri ga zabe da kuma kyakkyawan tsarin ci gaban Al’umma Inji Sanatan.

A nawa bangaren Inji Sanatan yace a taron, na jaddada bukatar hadin kai a matsayin wani muhimmin sharadi na ci gaban babbar jam’iyyar mu. Dole ne mu shiga cikin jerin tare da yunƙurin tattara mambobi. Dole ne muyi hakan cikin karfin gwiwa da alfahari.
Gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Nasir El-Rufai da ta ke gabatarwa. A zahiri ta zarce tsammani. An ba da fifiko kan ilimi, bunkasa ababen more rayuwa, noma da kiwon lafiya. Alkarya ta ci gaba ta daukaka sosai.
Tare da waɗannan nasarorin da ba za a iya musultawa ba, tabbas mutanenmu za su yi yunkuri domin damar yin rajista a babbar jam’iyyarmu.

A Karshe Sanatan Yace suna sa ran Samun Karin masu Rijistar sama da mutun milyan Daya Zuwa biyu…

Leave a Reply