Ku kawo mana korafin duk wata Matsalar ku Sakon Sanata Ahmad Lawan ga ‘yan Nageriya.

Spread the love

Shugaban Majalisar Dattawa Nageriya, Ahmad Lawan ya bukaci dukkan ‘yan Nijeriya da su kai duk wani korafinsu ko wanne irin ne ga Majalisarmu ta Dokokin Kasa, musamman ma yanzu da aikin sake duba kundin tsarin mulki ke gudana.

Lawan ya bayyana hakan ne a jiya lokacin da tawagar kwamitin jihar Enugu kan kirkirar jihar Adada suka ziyarce shi a majalisar kasa.

Tawagar wacce ta hada da tsohon Ministan yada labarai da kuma tsohon Shugaban Janar na kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Cif John Nnia Nwodo, karkashin jagorancin Cif Vita Abba.

“Wannan game da kirkirar jihar Adada ne. Amma akwai sauran wasu damammaki da yawa don inganta rayuwar mutanenmu ta hanyar gyara tsarin mulki.

“Don haka, ina amfani da wannan damar in yi kira ga‘ yan Nijeriya wadanda suke matukar jin dadin wasu batutuwa – yadda muke rayuwa tare, yadda muke tsare mutanenmu da duk wani abin da ke karkashin kasa wanda ‘yan Najeriya ke matukar ji da shi, da cewa tsarin mulki ya kamata ya samu ko bai kamata ba.

“Wannan shi ne lokacin da za a yi amfani da wannan damar domin zuwa Majalisar Tarayya don gabatar da kara. Mun zo nan ne don ‘yan Najeriya,” in ji Lawan.

Leave a Reply