Kungiyar Boko Haram ta kafa sabbin sansanoni a jihohin Yobe da Adamawa.

Spread the love

Wata majiyar tsaro ta lissafa wasu sabbin sansanonin maharan kamar kananan hukumomin Tarmuwa da Yunusari na jihar Yobe

Wasu rahotanni daga kafofin tsaro na zargin ‘yan ta’adda sun kafa wasu sabbin sansanoni a wasu sassan jihohin Yobe da Adamawa.

An gano cewa ‘yan ta’addan sun kafa maboya a Geidam da wasu sassan jihar Yobe.

Wata majiyar tsaro ta lissafa wasu sabbin sansanonin maharan kamar kananan hukumomin Tarmuwa da Yunusari na jihar Yobe; Mubi, Madagali da kananan hukumomin Gombi na jihar Adamawa.

A halin da ake ciki, a ranar Talata, wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne na kungiyar Boko Haram sun kai hari a karamar hukumar Geidam da ke jihar Yobe, inda suka yi awon gaba da wasu ma’aikatan hukumar Kwastam na Najeriya.

‘Yan ta’addan da ake zargi sun shiga garin ne da misalin karfe 5:30 na yamma ta hanyar Geidam Mane Shuwa Road kuma sun yi aiki na kimanin awanni biyu.

An ce sun fasa cikin shaguna da shagunan sayar da magunguna, sun wawushe kayan abinci, sun saci magunguna masu yawa tare da kona motar daukar marasa lafiya ta babban asibitin Geidam.

An tattaro cewa duk da cewa babu wani farar hular da ya rasa ransa, amma wata majiyar tsaro mai tushe, wacce ta yi magana da jaridar The PUNCH a Damaturu, ta ce, “‘Yan ta’addan, wadanda ke gudanar da ayyukansu a wadannan yankuna, tun daga lokacin sun tilasta wa wasu mazauna kauyukan ficewa daga gidajensu suka koma ga ‘yan uwansu a garin Geidam don aminci.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda reshen jihar Yobe, Abdulkarim Dungus, ya tabbatar da harin a kan Geidam.

Ya kuma bayyana cewa wasu mahara sun sace jami’ai uku na hukumar ta NCS, wadanda aka tura kwanan nan zuwa Yobe daga jihar Bauchi bayan da suka bar garin.

Leave a Reply