Gwamnati ta San duk inda ‘yan Ta’adda suke Kuma tana kallonsu ~Sheikh Gumi.

Spread the love

Fitaccen malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi ya zargi gwamnatin Najeriya da sanin maboyar makiyaya da ‘yan fashi.

Gumi ya ce gwamnatin tarayya tana zakulo ‘yan fashin da makiyaya ta hanyar hangen nesa.

Malamin ya yi wannan zargin ne a wani shiri na gidan Talabijin na Channels, Siyasar Yau.

Gumi ya ce gwamnati na yin taka-tsan-tsan saboda ta fahimci cewa hanyoyin da ake bi a baya na kashe ‘yan fashi sun faskara

Ya jaddada cewa tunkarar ‘yan ta’addan yana haifar da Karin ta’addanci daga cikin’ yan fashin.

Da yake amsa yadda ya gano tare da tattaunawa da ‘yan fashi yayin da gwamnati ta Gaza yin Haka, Gumi ya ce: “(Gwamnati tasan inda (‘yan fashi suke Kuma suna kallon su ta hanyar na’urar kallon nesa domin sojoji sun koyi darasi.

Hanyar farko da suka fara, lokacin da suka shiga suka fara kashewa- sun fahimci cewa ba daidai bane kuma suna haifar da wasu ‘yan ta’addan ne Yanzu kunga ai sunyi hankali.

A halin yanzu, Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ya ce gwamnati ba za ta iya lalata gandun dajin da ‘yan fashi ke amfani da shi a matsayin maboya don aikata muggan laifukansu ba.

Mohammed ya yi ikirarin cewa zai shafi yanayin halittar ne idan gwamnati ta yanke shawarar lalata gandun dajin da ‘yan ta’addan suke.

Leave a Reply