Labarai

Ha’dawar Kwankwaso da Obasanjo ba ta ba wa Tinubu tsoro ba – APC

Jam’iyyar APC mai mulki ta ce ba ta jin tsoron ziyarar da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso, da tsohon gwamnan Jihar Cross River, Donald Duke, suka kai gidan tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, da ke Abeokuta, Jihar Ogun, domin tattauna makomar siyasar Najeriya.

A cikin makonnin da suka gabata, an samu muhawara da ake yi kan zaɓen shekarar 2027, bayan da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya yi kira da a sake zaɓar Shugaba Bola Tinubu karo na biyu.

A cewar Akume, ba za a samu gurbi a fadar Shugaban Ƙasa ba har zuwa shekarar 2031, bayan Tinubu ya kammala wa’adinsa na biyu.

Sai dai jam’iyyun adawa ba su amince da wannan ba, inda suke nanata cewa za su kawar da APC daga mulki nan da shekarar 2027.

Duk da cewa ba a bayyana cikakken bayani kan abin da suka tattauna ba, wasu majiyoyi da ke kusa da shugabannin sun nuna cewa taron ya kasance wani yunkuri na tsara dabaru domin zaɓen 2027.

Sai dai, yayin da ya ke mayar da martani kan wannan batu a wata hira da The PUNCH a jiya Lahadi, Daraktan Yaɗa Labarai na APC mai mulki, Bala Ibrahim, ya yi watsi da taron a matsayin barazana ga ci gaban APC.

Ibrahim ya yi alfahari da cewa martabar siyasa da tasirin Tinubu a siyasar zamani sun rinjayi ‘yan adawa da tsofaffin shugabanni.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button