Kamar dai yadda aka saki bidiyon Dala na Ganduje Baffa Bichi Yasha Alawashin sakin bidiyon hujja kan Kwankwaso da Gwamna Abba.


Tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano, Abdullahi Baffa Bichi, ya yi barazanar fallasa gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf da ubangidansa, Rabiu Kwankwaso “a lokacin da ya dace”.
Mista Bichi ya yi magana a karon farko tun bayan tsige shi daga mukaminsa tare da wasu kwamishinoni biyar da gwamnan ya yi a watan Disamba 2024.
Da yake yiwa magoya bayansa jawabi a ranar Alhamis jim kadan bayan dawowarsa daga Saudiyya, tsohon SSG ya sha alwashin fallasa tsoffin abokan siyasarsa, yana mai cewa yana da wasu takardu, bidiyo da bayanan murya.
Dangane da Gwamna Yusuf da Kwankwaso, Mista Bichi ya bayyana mutanen biyu a matsayin shugabanni mayaudara da Cin amana
“Na yi farin ciki da na gama aikina cikin kwanciyar hankali. Kamar yadda kuka sani, wannan ba shine lokacin da ya fi dacewa don yin magana ba, amma a lokacin da ya dace za mu fallasa su don mutane su fahimci irin mutanen da suke.
“Ba mutane masu amina bane… Suna da yaudara sosai. Ba su san komai ba sai ha’inci da cin amana. Ba mutanen da za a amince da su ba ne.
“Mun rubuta komai tun daga rubuce-rubucen shaida zuwa sauti da bidiyo,” in ji shi a cikin wani jawabi da ya yi wa magoya bayansa.
Tun kafin a kore shi a matsayin SSG, reshen jihar New Nigeria People Party, NNPP, ta dakatar da shi bisa zargin rashin biyayya ga jam’iyyar da shugabancinta.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa Mista Bichi ya samu sabani da jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso, bayan da ya jagoranci wata kungiyar siyasa, Abba Tsaya da Karka a asirce, ya yi kira ga Mista Yusuf ya raba gari da ubangidansa.
