Dalilan Da Sukasa El-Rufa’i Yahana Sallah A Kaduna.

Spread the love
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-rufa’i

Daga Muktar Onelove Kaduna.

Zamu Cigaba Da Bawa Mutane Hakuri Na Zaman Gida, Kuma Muna Godiya Ga Al’ummar Jihar Kaduna.

Wadannan Matakan Da Muka Dauka Sune Mafita A Kaduna. Duk Mace-macen Da Ake Samu A Arewacin Najeriya Duk Covid 19 Ce, Kawai Ba A So Afada Ne.

Shi Wannan Ciwon Bai Da Kafa, Daukoshi Akeyi, Tabbas Idan Kafita Zaka Samu.

Ni Gwamna Sai Da Nakwana Tara Ban San Inada Ciwon Ba, Babban Hatsari Ne Abar Mutane Sutaru Waje Daya, Shiyasa Mukace A Daina Sallah.

Tun Da Ciwon Nan Yazo Mutum Biyu Ne Sukazo Dashi, Daya Daga Kano Dayan Kuma Daga Kasashen Ketare. Sauran Kuma Almajirai Ne Da Sukazo Daga Kano.

Ni El-Rufa’i Ranar Sallah Zanje Hanyar Kano Natare Hanyar, Babu Wanda Zaizo Yawon Sallah Kaduna Daga Kano, Zan Tsaya Daga Safe Har Yamma A Bakin Tirin Kano.

Ni Ina Tsoran Kano Sosai, Wani Dan Zariya Daga Kano Ya Dauko Ciwon, Ya Shafawa Yaranshi.

Sallah Ayi A Gida Babu Maganar Zuwa Masallaci, Babu Maganar Zuwa Idi, Ziyara Ayi A Waya, Yawon Sallah Ayi A Gida. Inji Gwamna El-Rufa’i.

Leave a Reply