Dalilin da ya sa na ziyarci garin Daura duk da rashin tsaro a Najeriya – in ji Buhari.

Spread the love

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da ya sa ya ziyarci mahaifarsa ta garin Daura a jihar Katsina yayin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Idan baku manta ba lokacin da shugaban kasan ya kasance a jihar Katsina, ‘yan bindiga sun sace sama da daliban makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati 300 a Kankara.

Rashin ziyartar wurin da lamarin ya faru ya jawo kakkausar suka daga ‘yan Najeriya wadanda ke mamakin dalilin da ya sa ya ziyarci mahaifarsa cikin rashin tsaro a kasar.

Shugaban ya bude ne a kan dalilin ziyarar tasa yayin da yake maraba da daliban daga garkuwar.

Ya ce, “Kullum na kan zo garin ne saboda na rantse da Alkur’ani mai girma cewa zan kiyaye tsarin mulkin kasa, saboda haka dole ne in mika mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023 ga gwamnati mai zuwa.

“Don haka, idan Allah Ya tsare min rai, babu shakka zan dawo gida. Wannan ya sanya ziyarar da na kawo gida. ”

Dangane da batun rashin tsaro, Buhari ya ce har yanzu hukumomin tsaro suna da sauran aiki.

“Wannan aikin su kenan. Sun sanya hannu a kanta. Ko suna so ko basa so, dole ne su samar da tsaro ga kasarnan, ” in ji shugaban.

Leave a Reply