Duk wanda yayi Yaki domin kabilanci bashi tare da Annabi Muhammadu SAW ~Dr Isa Ali Pantami

Spread the love

A daidai Lokacin da Rahotanni ke nuna da Cewa a kalla Sama da hausawa mutun goma 10 ne ake Zargin kabilar yuruba sun kashe a jihar Oyo yayinda Kuma Sama da mutun saba’in Suka Samu Raunika tare da bacewar mutun talatin 30 shi kuwa ministan Sadarwar Zamani Sheik Dr Ali Isa Pantami tunatar da Al’umma yayi hadisin Manzon Allah S.a.w Kan illar Nuna Kabilanci…

Ga hadisin kamar Haka…

عن جبير بن مطعم أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال ليس منا من دعا إلى عصبية وليس منا من قاتل على عصبية وليس منا من مات على عصبية

5121 سنن أبي داود

Jubayr bn Mut’im ya ruwaito cewa: Manzon Allah, tsira da aminci su tabbata a gare shi, ya ce, “Bashi a daga cikinmu kira zuwa ga kabilanci. Bashi daga cikinmu duk wanda ke yin yaki saboda kabilanci. Ba ya daga cikinmu da ke mutuwa ta hanyar kabilanci. ”

Daga : Sunan Abī Dāwūd 5121

Sahih mai daraja (ingantacciya) bisa ga As-Suyuti

Allah ka tseratar damu daga fushinsa !!!

  • Ahmed Adetola-Kazeem
  • Shafin Muslims News Nageriya ne suka wallafa shi Kuma Dr Ali Pantami ya rabashi izuwa shafinsa na Facebook.

Leave a Reply