
Ahmed T. Adam Bagas
Sanata Mai wakiltar Gabashin Neja Muhammad Sani Musa 313, Ya yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, da Ya Kirkiri Barikin Soja ko Sansanonin Soji a Yan Kunan Kananan Hukumomin Shiroro, Rafi, Munya Da Suke Fama da Tashin Hankula.
Yan kunan da Suke Gabashin Jahar Ta Neja Suna Fama da Hare Haren Yan Bindiga Wanda a Cikin Makon da ya gabata ma Yan Ta’addan sunci Karensu Ba Babbaka Inda Suka Kashe mutane 15 Sukayi Garkuwa da mutane 8 Mutane sama da 2000 Suka Gudu sukabar Muhallinsu a Yankin.