‘Yan Majalisar Wakilan Kasarnan Sun Amincewa Shugaban Kasa Muhamadu Buhari Ya Ciyo Bashi.

Spread the love

Daga Miftahu Ahmad Panda.

A jiya Talata ne dai Majalisar Wakilan ta Najeriya ta Sahalewa Shugaban Kasa Muhamadu Buhari a bisa kudirinsa na Ranto Zunzurutun Kudaden da Suka Kai Dalar Amurka Billion 22.799.

Tunda Fari dai Kwamitin da Majalisar Wakilan ta samar kan Ciyo Bashi tareda Yadda Za’a biya ne ya Bayyana Rahotonsa a zaman Majalissar na Jiya Talata, Bisa Jagorancin Shugaban Kwamitin Ahmed Safana, Wanda Dan Majalisane daga Jam’iyyar APC a Jihar Katsinan Dikko.

Safana Ya Bayyana cewar biyo Bayan Ciyo Bashin Dalar Amurka 22,898,446,773 da akayi a Watan October Shekarar 2019, Shugaban Kasa Muhamadu Buhari yasake Mikawa Majalisar Wakilan Bukatarsa ta su Sahale Masa domin yayo Rancen wasu Kudaden da Suka Kai kimanin Dala 17,065,496,773 daga Bankin Eximbank dayake a Kasar Sin Wato China,

Yakara da Cewar a Cikin Adadin Kudaden da Za’a Ciyo Bashin na Dalar Amurka Billion 22.799, A Bankin Eximbank Bank na Kasar Sin Za’a Ranto Mafi yawan Kudaden, Domin Kuwa Za’a Karbo Kimanin Dalar Amurka Billion 17.066 da Sharadin Cewar Za’a Biya Kudinne a Tsukun Wa’adin Shekaru 20, Sannan da Karin kaso 2.75 na kudin Ruwa,

Daga Cikin Ayyukan da za’ayi da Kudin dai sun Hadarda Kammala Layin Dogo daga Jihar Lagos Zuwa Kano, Sannan da Wani Karin Layin Dogon Shi kuma daga Port Harcourt Zuwa Enugu, Zuwa Makurdi, Zuwa Plateau Zuwa Maiduguri.

Leave a Reply