Yaki da ta’addancin Boko Haram Sarkin musilmi ya kalubalanci Rundunar Sojojin Nageriya.

Spread the love

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III ya jagoranci majalisar Sarakunan gargajiya na Nigeria zuwa birnin Maiduguri jihar Borno inda suka gana da Maigirma gwamna Farfesa Babagana Umara Zulum (Khadimul Ummah)

Sarkin Musulmi Abubakar Sa’ad III a matsayinsa na tsohon soja wanda yayi ritaya a mukamin Janar kafin ya zama Sarkin Musulmi, ya kalubalanci rundinar sojin Nigeria akan dalilin da ya hanata mamayar Tafkin Chadi da Jejin Sambisa inda maboyar ‘yan ta’addan Boko Haram yake

Sarkin yace; Na karanta jawabin da Gwamna Zulum yayi akan cewa ya kamata sojoji su isa inda manyan sansanonin ‘yan Boko Haram yake a Tafkin Chadi da Sambisa domin a gama da su, Maigirma Gwamna ina tabbatar maka da cewa shekaru sama da 40 lokacin da nake aikin soja ina da mukamin Laftanar an kaini Tafkin Chadi nayi shekaru kusa 3 a garin Baga, bataliyar rundinata mu kanyi hadin gwiwa da bataliyar sojojin da suke Monguno da Maiduguri, duk bayan wata 6 mu kan hadu mu tsara rawar daji mu mamaye yankin Tafkin Chadi dake fadin iyakar Nigeria

Na kasance kwamandan yakin bataliyar sojoji na garin Baga a lokacin ina da mukamin Laftanar, ina da zanen taswirar yankin Tafkin Chadi gaba daya, muna da tsibiri guda 36 na yankin Nigeria a Tafkin Chadi, mun mamaye tsibiri guda 16, babban tsibiri a lokacin shine tsibirin Nasara, bataliyarmu ta tabbatar da tsaro a lokacin, don haka a yanzu ban san dalilin da yasa sojojin Nigeria ba zasu iya mamayar Tafkin Chadi da Jejin Sambisa ba, matukar muna bukatar zaman lafiya to ya zama wajibi mu mamaye wadannan yankuna, matukar muna son zaman lafiya ya zama dole mu kori ‘yan ta’adda daga wadannan yankuna, babu wani dalili da zai hanamu aiwatar da hakan, inji mai Alfarma Sarkin Musulmai

Sarkin Musulmi ya kara da cewa wannan shine karo na farko da majalisar Sarakunan gargajiya na Nigeria ta kawo ziyara Borno domin gabatar da jawabi wa dukkan al’ummar Nigeria, kashe kashe sunyi yawa, ta’addanci, garkuwa da mutane ya mamaye ko’ina fadin kasa, lokacin da nazo Maiduguri bude Masallaci gwamnan Zulum yana ‘dan takaran gwamna, wannan shine karo na farko da nazo Maiduguri tun bayan da ya zama Gwamna, Alhamdulillah muna ganin kokarin da yake yi, ina yawan tattaunawa ta waya da Shehun Borno yana fadamin halinka na kirki, muna da kyakkyawan zato na alheri a kanka, kana kokari, amma yanzu ka fara

Yaci gaba da cewa; Na san Maiduguri tun ina da kuruciya, anan na girma, lokacin da nake aikin soja nayi shekaru kusan 3 a barikin sojoji dake garin Bama, barikin sojoji da nayi rayuwa a gidan soja da mukamin Laftanar shine barikin da ‘yan ta’addan Boko Haram suka ruguza sula kona, ya zama wajibi a tashi tsaye a isa inda Boko Haram suka buya a kawar da su, inji Mai Alfarma Sarkin Musulmai

Alhamdulillah Mai Alfarma Sarkin Musulmai ya sauke nashi nauyin, ya fadawa rundinar sojin Nigeria gaskiya, ya rage nata ta dauki shawaran ko tayi watsi da shi

Muna rokon Allah Ya sa rundinar sojin Nigeria tayi amfani da shawaran tsohon Janaral Sarkin Musulmin Nigeria Amin daga datti datti

Leave a Reply