Shugaba Buhari ya fasa halartar gayyatar da majalisar dokokin Najeriya ta yi masa don yin bayani dangane da halin rashin tsaro da ake fama da shi a Najeriya.
Shugaba Buhari ya bi shawarar da gwamnonin APC suka bashi ne na janye halartar gayyatar da majalisar dokokin Najeriya ta yi masa bayan sun gana da shi a ranar talata a fadarsa da ke babban birnin tarayya Abuja.
Gwamnonin na APC sun nemi shugaba Buhari da kada ya je majalisar dokokin ta Najeriya ne duba ga yadda suka tattauna yadda za a shawo kan matsalar tsaron kasar wanda suka ce hakan ma ya wadatar ba sai ya je majalisar dokokin don yin wani bayani ba kuma.
Daga Kabiru Ado Muhd