Kasuwanci
Zamu bude iyakokin Najeriya a kwanan nan, in ji Gwamnatin Tarayya.
Ministar kudi kasafi da tsare tsare ta Najeriya Hajiya Zainab Shamsuna Ahmad ta ce nan bada dadewa ba gwamnatin tarayya zata bude iyakokin Najeriya.
Zainab shamsuna ta bayyana haka ne a wajen taron tattalin arzikin kasa Wanda aka gudanar a Abuja.
Zainab shamsuna tace an kafa wani kwamiti dayake duba yiwuwar hakan, kuma an cimma matsayar bude iyakokin Na Najeriya.
Zainab Shamsuna tace an cimma matsayar ne bisa tattaunawa da kwamitin yayi da kasashen dake makwabtaka da Najeriya kuma bayanansu ya nuna cewa sun shiga taitayinsu tare da bada tabbacin kiyaye sharudan da Najeriya zata gindaya musu.
Zainab Shamsuna tace don haka yanzu shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ake jira ya sanya ranar da za a bude iyakokin Na Najeriya.

