Labarai

Na yi farin ciki cewa wahalar da suka sha ta zo karshe mai kyau ba tare da wani matsala ba, sakon murnar Buhari na dawowar ‘yan matan Jangebe.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna farin cikinsa na dawowar Ɗalibai Mata na makarantar Gss Jangebe ta jihar Zamfara wadanda ‘yan ta’adda suka sace a makon da ya gabata.

Shugaban ya bayyana hakan ne ta shafinsa na Twitter, inda yace
“Na shiga cikin dangin da abin ya shafa da kuma mutanen jihar Zamfara wajen yin barka da nuna murna da sakin daliban GGSS Jangebe da aka sace.

Wannan labarin ya kawo farin ciki mai yawa. Na yi farin ciki cewa wahalar da suka sha ta zo karshe mai kyau ba tare da wani matsala ba.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button