Rahotanni

Rayuwar Alh Ahmadu Haruna Danzago

1-Dan Canji:

Marigayi Alh Ahmadu Haruna Danzago ya yi shura a fannin harkar hada-hadar canjin kudaden kasashen waje, yana daya daga cikin yan canji da suka kafa wannan harkar a fadin kasar nan- da hakan tasa har ya taba zama Shugaban Yan kasuwar Canjin Kudade waje na Jihar Kano (Kasuwar WAP). Mutane da dama basusan cewa ita kanta kalmar “Chairman” da Ke kiransa da ita ba, ba wai a harkar siyasa ya same ta ba, ta samo asali ne sakamakon Chairman na Yan Canji da yayi…

2-Dan Siyasa:

Dan Zago dan siyasa ne tin 1979 ake gwagwarmayar siyasa da shi a fadin kasar nan.

A lokacin siyasar Jamhuriyya ta biyu, Dan Zago ya kasance dan Jam’iyyar PRP. A Jamhuriyya ta uku kuma, ya goyi bayan Jam’iyyar NRC wacce ta baiwa Arc. Kabiru Ibrahim Gaya daman zaman Gwamnan Jihar Kano. A shekarar 1998, Dan Zago ya zama daya daga cikin Manya a Jam’iyya APP, wacce daga bisani ta samar da Malam Ibrhaim Shekarau a Matsayin Gwamnan Jihar Kano a shekarar 2003 bayan ta zama Jam’iyyar NNPP. Kafin sannan, a shekarar 2002 ne su ka shigo da Buhari Siyasa karkashin Jagorancin Marigayi Alh Wada Nas.

Danzago ya kasance daya daga cikin wadanda suka kafa Jamiyyar CPC karkashin Sanata Rufai Sani Hanga. Inda ya zama Shugabanta na shiyyar Arewa Maso Yamma, sannan ya zama Shugabanta na Jihar Kano-kafin daga bisani a narkar da ita cikin wasu Jam’iyyu da suka samar da Jam’iyyar APC me mulkin Nigeriya halin yanzu.

3-Harkar Kamfanoni da Masana’antu.

Marigayi Amb. Alh. Ahmadu Haruna Zago, mutane da dama sunfi saninsa a abinda ya shafi siyasa, amman basu san cewa gogaggen masanin tafiyar da harkokin kamfanoni da masa’aantu bane. Ya kasance babban Chairman na Kamfanin ASPIRA masu yin sabulai da OMO na VIVA, shine kuma babban Darkata a kamfanonin Mr- Lee da ya hada da babban kamfaninsa dake Jagona da kuma Kamfanin Rodi dake Unguwar Sharada.

4- Samar da VISA.

Marigayi Dan Zago, mutum ne da ya dade yana harkar samawa matafiya kasa mai tsarki Visa, wanda hakan yasa yake da alaka mai kyau tsakaninsa da Kasar ta Saudiyya, da hakan ya sa har ya kan zama mai shiga tsakani da Gwmantin Saudiyya da kuma ta Jihar Kano da ma wasu Jihohin, musamman idan ana son kulla wata alaka a tsakanin kasashen biyu. Ance a shekarun baya, shi ne mutum na farko da Kasar Saudiyya ta amincewa zai iya samawa dan Nigeria ko a ina yake Visar shiga kasar har na shekara daya.

5-Alaka tsakanin Larabawa da yan China.

Tin bayan rasuwar Marigayi Gadaliman Kano, Alh. Tijjani Hashim, babu wanda ya zama baya goya marayu tsakanin mutanen kasar China da Larabawa mazauna Jihar Kano, sai Dan Zago- Kuma hakan ya samo asali ne saboda tsohuwar alakarsa da Marigayi Galadiman Kanon. Ance tin Galadima na raye, idan yan China ko Larabawa sun kawo masa korafi game da wani abu da akai musu da shi kadai ke iya sa baki a warware abun, sai ya ce su bari Dan Zago yazo, wato lokacin girma ya kama Marigayi Galadiman, amman da yake yasan Dan Zago mutum ne mai jajircewa, shi kadai ya yarda zai iya shige musu gaba domin warware musu duk wata matsala dake damunsu a nan Jihar Kano dama wasu sassan kasar nan.

6-Gaskiya da rikon Amana.

Daya daga cikin abunda yake hada Dan Zago da wasu mutane rigima shine, rashin gaskiya. Domin duk sharrin da za kaiwa Danzago, baka isa kace an hada baki da shi an ci amanarka ba, ko kuma ace ka dora shi ya shugabaci wani abu a samu cin amana a ciki. Ko mukami aka bashi a Gwamnati, in kaji wasu na kunkuni a kansa ba wani abu bane, sai kawai shi ba zai ci kudin Gwamnati ba, kuma duk yadda kuke da shi, kai ma ba zai taba bari kaci ba. Dan Zago baya goyon bayan mutum indai ya aikata wani abu na rashin gaskiya, ko da kuwa dansa ne na cikinsa..

7-Kyautatawa Yan Uwa.

Duk wani dan uwa ga Dan Zago, tabbas dole ya yi kuka da rashin sa, saboda Dan Zago mutum ne mai son yan uwansa, baya kosawa da bukatunsu a duk lokacin da suka zo masa da su. Da zarar ance watan Azumin Ramadan ya tsaya, haka zai rabawa yan Garinsu Kayan Azumi domin suje su yi hidimar Azumi. Haka kuma duk Sallah Babba, zai bada miliyoyin kudi aje kasuwar Kauye, a siyo kosassun raguna don ya rabawa duk yan uwansa na kauyensu Zago, a Karamar Hukumar Danbatta, da kuma mazauna Kano kowa daya suma su je su yi layyar salla.

8-Ciyar da Bayin Allah.

Duk wanda yake zuwa gidan Dan Zago daga bayan Magariba, yasan zai gasgata ni cewa, za’a fito da abinci mai rai da lafiya aci ako shi, da yagama cewa, abincin gidansa da ake fitowa da shi ya faraiwa mutane kadan, sai yasa aka samo masa wadanda suka iya dafa abinci, inda ake ware kudi kullum sai an dafa abinci a wani gidansa dake kusa da wanda yake ciki, kawai dan mutane dake zuwa gidansa su ci su koshi. Kuma duk irin abinci da za’ai masa ya ci, irinsa kowa zai ci.

Sannan duk Azumi tin daga farkon Azumi har a gama, ana shirya abinci iri daban-daban dan yin buda baki da shi a gidansa..Haka mutane da dama ke zuwa ayi buda baki da su.

9-Mutunta Abokan Siyasa.

Dan Zago baya jefar da masoyinsa a Siyasa, sai dai kai ka rabu da shi. Hakanne yasa duk azumi sai ya rabawa Shugabannin Kungiyarsa ta Zago Akida na Kananan Hukumomi 44 na Jihar Kano kayan Azumi da ya hada da Buhun Shinkafa kowa daya tare da kudi dan su ma su sa sawa iyalansu farin ciki lokacin ibadar Azumi.

10-Uba Na Gari.

Marigayi Dan Zago, ya kasance mutum mai sadaukar da arzikin da Allah ya yi masa ga iyalansa banda hidimar da yakewa sauran al’ummar gari. Allah ya albarkace shi da yaya da yawa- maza da mata, Kuma sama da mutum 20 maza da mata na da aure a yanzu haka. Sannan cikin yayansa, akwai kusan 20 a ciki da suka gama karatun Digiri a makarantun gida da na kasashen waje. Dan Zago bai taba nemawa dansa aiki a Gwamnati ba, duk kuwa da tsahon alakar da yake da ita da Gwamnatoci da dama a kasar nan.

11-Siriki Na Kwarai!

Duk wanda yasan waye Marigayi Alh. Ahmadu Dan Zago, lallai zai baka labarin cewa samun siriki kamarsa a wannan zamanin gaskiya sai anyi bincike na gaske. Saboda duk wanda ya auri yarsa, tabbas zai sha mamaki. Zai maida ka kamar shi ya haife ka, duk lokacin da yarsa da ta haihu ko dansa da matarsa ta haihu, in sha Allah sai an kai musu katon rago don suyi shagalin suna. Sannan duk Sallah sai an kaiwa duk Da ko Yarsa dake da aure rago koda ko mijin yafi dan Zagon tarin dukiya.

Sannan duk irin bukatar da yarsa mace tazo masa da shi, zai kawar da ita nan take ba tare da la’akari da cewa mijinta ma zai iyayi mata ba. Idan ma matsalar Mahalli ce, dan Zago zai baiwa yarsa gida yace ta zauna ita da mijinta.

Kuma duk lokacin da Dansa namiji zai aure, sai an gina masa katafaren gida an kuma cika shi da kayan alatu…duk saboda su samu nutsuwa da kwaciyar hankali a zamantakewar aure. Babu wani dansa guda daya da ya taba zama a gidan hawa idan yazo zai aure.

Marigayi Dan Zago ya rasu yana da shekaru 75, an haife shi a shekarar 1950, kuma ya bar mata hudu, yaya 37, tare da jikoki da dama.

Allah ya yi masa Rahama ya sada shi da Annabin Rahama. Allah ya hada masa kan iyalansa tare da sauran yan uwa da abokan arziki baki daya.

Ameen…

Hassan Auwalu Muhammad
13-02-2025

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button