Tinubu Ya Shiga Cikin Jerin Mutane 100 Mafi Tasiri A Duniya Na Shekarar 2023

An jera Tinubu tare da Shugaban Amurka, Joe Biden, da sauransu.
Zababben shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya kasance cikin jerin mutane 100 da suka fi tasiri a shekarar 2023 da mujallar Time ta fitar.
Jerin shekara-shekara na Mujallar Time na mutane 100 mafi tasiri a duniya suna gane mutane don canza duniya, ba tare da la’akari da sakamakon ayyukansu ba.
Jerin 2023 da aka fitar ranar Alhamis ya rarraba mutane zuwa majagaba, shugabanni, titan, masu fasaha, masu kirkire-kirkire, da gumaka.
Tinubu, wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a Najeriya a ranar 25 ga watan Fabrairu, an saka shi ne tare da shugaban kasar Amurka, Joe Biden; Shugaban Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva; Uwargidan shugaban kasar Ukraine, Olena Zelenska; a tsakanin sauran shugabannin duniya.
Rahoton ya bayyana Tinubu, wanda za a kaddamar da shi a ranar 29 ga Mayu a matsayin “Dan takarar da ya dade a siyasance”.
Rahoton ya kuma ce da alama Tinubu yana sane da gadon nasa da suka hada da “rikitattun rikice-rikice a cikin kasar da ta wargaje, da suka hada da cin hanci da rashawa, tada kayar baya na addini, da karancin kudi, man fetur, da wutar lantarki a cikin tabarbarewar tattalin arziki”.