Labarai

Da dumi’dumi: An Gano yadda Ganduje ya sace bilyan 100bn na kananan hukumomi.

Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) dake jagoranci gwamnati mai zuwa a jihar Kano ta yi ikirarin cewa Gwamna mai barin gado Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC ya karkatar da kudaden kananan hukumomi Naira biliyan 100.

Wannan ikirari ya fito ne daga bakin wani dan kwamitin karbo kadarorin jam’iyyar NNPP, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, a wani taro da aka gudanar a Kano.

Takardun da aka gano sun nuna karara yadda aka karkatar da Naira Biliyan 100 daga Baitulmalin Karamar Hukumar Kano zuwa wasu asusu na kashin kai, wannan ya kaucewa wasu karkatar da akalar da muka gani wajen gudanar da bincikenmu,’’ inji Gado a daidai lokacin da gwamnati mai jiran gado da gwamnatin jihar. Gwamnati mai barin gado tana takun saka kan batun mika mulki.

Zargin na baya-bayan nan ya biyo bayan kiran da shugaban kwamitin mika mulki na jihar Kano, AB Baffa, PhD, ya yi a ranar Alhamis, ga masu fafutuka da su fito da duk wani bayani da ya dace dangane da shekaru takwas da Ganduje ya yi.

Sanarwar da kwamitin ya fitar ta wani bangare na cewa, “Kwamitin mika mulki na NNPP, GTC wanda mai girma Gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf, zababben gwamnan jihar Kano yana gayyatar jama’ar da abin ya shafa wadanda suke da duk wani bayani da zai taimaka wa gwamnati mai jiran gado ta kara fahimtar abubuwan da suka faru a cikin shekaru Takwas da suka gabata (2015-20231) don mika irin wadannan bayanai. a rubuce zuwa ga Sakatariyar GTC dake fadar shugaban ta a Tahir Guest Palace No.4 Ibrahim Road Kano.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button