Labarai

‘Yan Nageriya ku cigaba da hakuri domin Tinubu ya gaji mummunan matsalar tattalin arziki daga Gwamnatin Buhari ~Cewar Oshiomhole

Sanata mai wakiltar mazabar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya ce gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta gaji wani mummunan hali na tattalin arziki.

Oshiomhole ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin wata tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan sun rufe Kofa sun ganawarsa da mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima a Abuja.

A cewar tsohon shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta kasa, wasu daga cikin hukunce-hukuncen da gwamnati mai ci ta dauka su ne matakin farko da inganta tattalin arzikin kasar.

Ya kara da cewa, shugaba Tinubu da mataimakinsa sun nuna jajircewa da kwazo wajen ganin an dakile almundahanar kudaden tallafin da kuma babban bankin Najeriya (CBN), tare da yin kira ga ‘yan Najeriya da su yi hakuri.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button