Labarai
Da dumi’dumi: Shekarau ya jinjinawa Gwamna Abba Gida-Gida kan kokarin inganta Ilimi a jihar Kano.

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon Sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau, ya jinjinawa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Engr Abba Kabir Yusuf bisa ware kaso mafi tsoka ga fannin ilimi, da ya kai kaso talatin cikin dari na kasafin kuɗin shekarar 2024.
Malam Ibrahim Shekarau yace a tarihin jihar Kano babu wata gwamnati da ta taɓa ware kaso mai tsoka ga bangaran na ilimi haka.
Shekarau ya yi wannan tsokaci ne yayin wata ganawa ta musamman da
Rahma Radio da Talabijin a dangane da cikarsa shekara 68 a duniya.


