Labarai

Da dumi’dumi: Kungiyar kwadago NLC da Kungiyar ‘Yan kasuwa sun kira taro domin yanke hukunci kan tafiya Yajin aiki Mai zafi a duk fa’din Nageriya.

Shugabannin kungiyar Kwadago ta Najeriya da kuma kungiyar ‘yan kasuwa sun kira wani taro na musamman na majalisarsu ta zartarwa ta kasa.

Vanguard ta tattaro cewa mataimakin shugaban TUC na kasa, Tommy Etim ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a ranar Talata.

A cewar Etim, taron na neman duba yanayin yajin aikin ne biyo bayan cin zarafin da shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero ya yi.

Ana kuma sa ran taron zai sake duba yarjejeniyar fahimtar juna da Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Kwadago suka sanya wa hannu a ranar 2 ga Oktoba, 2023, bayan cire tallafin, wanda cibiyoyin kwadagon suka ce ya janyo wa ‘yan Najeriya “wahalhalun da ba a bayyana ba.

Ya ci gaba da cewa, “Za mu gudanar da wani babban taro daga zuwa a kowane lokaci daga yanzu. Hanyoyin da za a bi sun hada da rashin adalcin da aka yiwa comrade Ajaero, yajin aikin da aka shirya da kuma MOU da suka rattaba hannu da gwamnatin tarayya. Za a bayyana karin bayani bayan taron.”

Ku tuna cewa kungiyar kwadagon, a ranar Juma’a ta bayar da wa’adin kwanaki biyar kan kama Ajaero, da ‘yan sanda suka yi a Owerri, jihar Imo, ranar Laraba.

Kungiyoyin sun bukaci a sauya kwamishinan ‘yan sanda a jihar tare da kama tare da gurfanar da mai taimaka wa gwamnatin da ake zargi da kai harin.

Sun kuma yi barazanar shiga wani mataki a fadin kasar idan ba a biya musu bukatunsu ba nan da kwanaki biyar daga ranar Juma’a.

‘Yan sanda sun kama Ajaero ne gabanin zanga-zangar da aka yi a jihar Imo a ranar Laraba. Shugaban yada labaran NLC, Benson Upah ne ya bayyana hakan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button