Labarai
Shugaba Tinubu zai bawa Tsofaffin Shugabannin Kasar Najeriya kulawa ta musamman da Naira Biliyan 13.8bn.

Gwamnatin Najeriya ta ware kudi naira miliyan 13,805,814,220 domin kula da tsofaffin shugabannin kasa da mataimakan shugaban kasa wa’yanda suka Gabata shugabannin kasa, manyan hafsoshin soji, shugabannin ma’aikata da suka yi ritaya, da sakatarorin dindindin, da shugabannin hukumomin gwamnati da ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya wannan ya kunshe ne a cikin kasafin kudi na 2024.
Wadanda za su ci gajiyar tallafin sun hada da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari, da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Namadi Sambo da Farfesa Yemi Osinbajo.

