Najeriya kasa ce da ta gaza samun Nasara kuma idan ba mu yi aiki ba mafi munin zai faru –Attahiru Jega
Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya yi gargadin cewa Najeriya kasa wacce ta gaza, don haka akwai bukatar shugabanni da ‘yan kasa su kiyaye tsarin domin hana “mafi muni na iya faruwa.
Jega, wanda ya jagoranci babban zaben shekarar 2015, ya bayyana cewa Najeriya na da “tsarin shugabancin kasa” wanda ba shi ne mafi kyau a duniya ba, yayin da ya yi kira ga shugabannin da su rage tsadar harkokin mulki.
Ya yi wannan jawabi ne a ranar Asabar a lokacin da yake gabatar da lacca a Jami’ar Jihar Bauchi, Gadau, mai taken, ‘Kiyaye makomar Nijeriya: Gabatar da walwalar jama’a da tsaro a lamarin kalubale.
Ya ci gaba da cewa, “Shugabannin mu da ke kan mukaman shugabanci, daga yanzu zuwa 2027, akwai bukatar mu hada kawunanmu wuri guda, mu yi tsarin da ya dace, bisa hujja na sake fasalin tarayyar Najeriya, kuma a raina babban abin da ya kamata mu yi shi ne mika wuya. mulki da albarkatu tun daga tarayya zuwa jiha da kananan hukumomi.