Shugaba Tinubu Yana Aiki tukuru domin hana Tattalin Arzikin Nageriya Durkushewa -Gwamna Uba sani


Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya yi gargadin cewa mutanen da muradin su ke da alaka da mulkin masu rinjaye suna aiki tukuru don dakile dimokuradiyyar kasar nan.
Gwamnan ya zarge su da murde ‘yan Najeriya tare da haifar da rashin hadin kai ta hanyar siyasantar da komai, ya kara da cewa ‘sun kasuwantar da kasarmu suna kuma bata mata suna a duniya.
Gwamna Uba Sani wanda ya bayyana hakan a wajen bikin bude taron Majalisar Watsa Labarai da Wayar da Kan Jama’a karo na 48, ya yi gargadin cewa ‘’Dole ne mu sa ido sosai tare da samar da dabarun sadarwa na zamani don dakile labaran da ke raba kan jama’a’
Gwamnan ya tunatar da taron cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya karbi mulki a wani mawuyacin lokaci a tarihin kasar nan domin ya gaji tattalin arzikin kasa gurbatacce
Gwamna Uba Sani ya bayar da hujjar cewa shugaban kasa yana da aikin da ba za a iya mantawa da shi ba na farawa da aiwatar da matakai masu nisa don hana tattalin arzikin Najeriya durkushewa.

