Femi Fani Kayode Ya Bada Hakuri Kan Zagin Da Yawa Dan jaridar Daily Trust.
Tsohon Ministan Sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode bayan cin zarafin da yawa wakilin jaridar Daily Trust a jihar Cross-River da hakan ya jawo cece-kuce ya bada hakuri.
Kayode ya zagi dan jaridar bayan da ya tambayeshi wake daukar nauyin rangadin ganin ganin ayyukan da yake a jihohi kusan 6. Mun ruwaito muku kungiyar ‘yan Jaridu ta Duniya, data Najeriya da Daily Trust da SERAP duk sun yi Allah wadai da abinda Femi yayi inda ‘yan Najeriya da dama suma suka rika caccakar sa a shafukan sada zumunta.
A baya yace yana nan kan bakansa saidai da safiyar yau ya bayyana cewa bayan shawara da masu bashi shawara ya janye zagin da yawa dan jaridar. Mun fahimci Kayode yace yana da abokai ‘yan jarida kuma yana girmama aikin dan haka ba zai yi abinda zai bata aikin ba.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
