Ilimi

An Bankado Malaman Firamare 2,286 Da Takardun Shedar Bogi A Jihar Neja.

Kwamitin binciken ma’aikata na shekara ta 2020 wanda Hukumar Kula da Ilimin Firamare ta Jihar Neja (NSUBEB) ta kafa, a jiya Litinin ya ce akalla malaman firamare 2,286 ke amfani da takaddun shaida Na bogi a fadin jihar.

Alhaji Ayuba Katako, Shugaban kwamitin ne ya bayyana hakan yayin gabatar da rahoton binciken na shekara ta 2020 ga shugabannin hukumar na NSUBEB a Minna.

A cikin watan Yuni ne hukumar gudanarwar ta kafa wani kwamiti na mutum shida domin ta binciki duka ma’aikatan koyarwa da wadanda ba na koyarwa ba na NSUBEB a duk fadin jihar dake da Kananan Hukumomi 25 na jihar.

Katako ya ce akwai ma’aikata 28,058 a makarantun firamaren da ke fadin jihar, ya kara da cewa 26,00 7 daga cikinsu an tantance su, daga cikin 23,721 da aka tantance kuma sun dace su yi aiki a SUBEB.

Ya lura cewa 2,286 daga cikin wadannan malaman makarantun firamaren suna amfani da takaddun shaida da ake shakku domin wasu daga cikinsu ba su iya karatu da rubutu ba.

Ya bayyana cewa akasarin wadannan takaddun shaida suna karatu ne a Cibiyar Koyar da Malamai ta Kasa (NTI)dake Kaduna kuma ba su yi daidai da takaddun shaidar da NTI take bayar wa Ba.

Katako, duk da haka, ya lura cewa kwamitin ya kuma gano har sai an karawa malamai girma, kuma a shiyyar A, malamai masu digiri na uku sune wadanda ke koyarwa a ajujuwa yayin da wadanda suke da Masters su ne a ofis.

Da yake maida jawabi, Dr Adamu Isah, Shugaban SUBEB na jihar, ya yabawa kwamitin kan gudanar da aikin yadda ya kamata, sannan ya ce hukumar za ta bi diddigin dokokin aikin gwamnati don yanke hukunci a kan wadanda aka samu da yin aikin Ba bisa ka’ida ba Inji Shi.

Ya kara da cewa duk malamin da bai iya rubutu ko karatu ba za a cire shi a matsayin malami kuma ya shiga wani fannin.

“Wadannan mutane za su tsinci kansu a matsayin masu shara, masu kula da yara da kuma wasu a ofisoshin kananan hukumomi daidai da karfinsu,” in ji shi.

Isah ya ce za su tuntubi cibiyoyin da ke bayar da wadannan satifiket din don tabbatar da sahihancinsu kuma duk wanda satifiket din ba na kwarai ba ne to za a dakatar da shi daga aiki.

Amma, ya bayar da tabbacin cewa za a aiwatar da aikin da ya dace kan rahoton kwamitin.

Hakanan, Alhaji Kabiru Abbas, Memba na II, ya yaba wa kwamitin kuma ya ce rahoton “ya kawo karshen duk wasu zarge-zarge da zage-zage daga jama’a”.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button