Rundunar Mayakan Sojojin Sama Sun Yiwa Yan Bindiga Ruwan Wuta A Katsina.
Hedkwatar tsaron Najeriya DHQ ta alanta nasarar sojin sama a jihar Katsina.
A harin da aka kai jiya, Sojin sun hallaka dimbin yan bindigan tare da ragargaza sansaninsu.
Sojin sun samun labarin kasancewar yan bindigan a wajen ne daga bakin mutane Rundunar mayakan saman Najeriya (NAF) karkashin atisayen Operation HADARIN DAJI sun samu nasarar ragargaza wani sansanin yan bindigan da suka addabi al’ummar jihar Katsina da kewaye.
Jami’an sun samu nasarar yin hakan ne a harin da suka kai ranar Talata, 13 ga Oktoba.
Hedkwatar tsaro ta bayyana cewa “an wargaza sansaninsu kuma an hallaka wasu yan bindigan kusa da Unguwar Ali-Kere a jihar Katsina.” A jawabin da hedkwatar ta saki a shafinta na Tuwita, ta ce “bayanai daga mutan gari ya nuna cewa akwai yan bindiga a wajen kuma sun kafa sansani.” “Saboda haka hukumar mayakan sama ta tura jiragen yaki da masu saukar angulu inda suka ragargaji wajen, cikin jawabin nasa. Daga Comr Haidar Hasheem Kano
