Ku kyale Zanga Zangar #Endsars ku zo muyi Yaqi domin Kafa kasar Biafra~ Dokubo Asari
Tsohon shugaban tsagerun Neja Delta, Alhaji Asari Dokubo ya yi kira ga jama’ar yankin da su manta da zanga-zangar adawa da cin zarafin ‘yan sanda da kuma fatattakar rundunar‘ yan sanda ta musamman mai yaki da fashi da makami, SARS a yanzu, sannan su mayar da hankali kan sake dawo da kasar Biafra. a ranar Lahadi, Asari ya yi jawabi ga mutanen Neja Delta da ke shiga zanga-zangar a fadin kasar, wanda ya ce bata lokaci ne. A cewarsa, babu wani abu da za a sake fasaltawa game da Najeriya,
yana mai dagewa kan cewa bata lokaci ne kawai don hada kai da Yarbawa a zanga-zangar #ENDSARS, ya kara da cewa mafita kawai ga ‘yan Niger Delta ita ce hada kai da Ogonis da Igbos da Efiks domin sake kafa kasar Biafra.
Ya ce hakan ya faru ne saboda babu wanda zai iya danne dan kabilar Ijaw din a Biafra. Asari ya ce abin da mutane suke bukata a halin yanzu shi ne ‘yanci na siyasa kuma duk wani abin da zai zo a lokacin da ya dace,“ hakan kuma zai baku damar ku mallake mai,



