Labarai
Ga Mai son Aikin N-Power Yana iya shiga ya cike fam din.
Gwamnatin tarayya ta bude sabon shafin da zai taimakawa tsaffin matasan N-Power dman neman tallafi da jari na babban bankin Najeriya CBN. Wannan shafi da ma’aikatar jinkai da walwala ta shirya tare da hadin kan CBN zai taimakawa wadanda aka cire daga shirin N-Power su shiga domin neman abubuwan alfanu da CBN ke da shi na tallafi, bashi da jari. A jawabin da Sakataren ma’aikatar,
Bashir Nura Alkali ya sake a madadin ministar, Hajiya Sadiya Farouq, ta yi kira ga matasan su shiga shafin domin sanya sunayensu saboda su samu shiga cikin duk wani shiri da CBN ta gabatar.

