Hukamar NDLEA ta gano ‘Yan wiwi Cikin ‘yan takarar kananan Hukumomi a Jihar Kano.
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta tantance akalla ‘yan takara 250 na jam’iyyun siyasa don shan kwayoyi a jihar Kano.
Yan takarar sun kasance ga zabukan kananan hukumomi da ke tafe a jihar.
Kwamandan hukumar ta NDLEA a jihar Kano, Dr Ibrahim Abdul, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Kano ranar Juma’a cewa ‘yan takarar sun fito ne daga kananan hukumomi 19 daga cikin 44 na jihar.
Abdul ya ce tantance ‘yan takarar mukaman ciyaman, mataimakin ciyaman da kansiloli ya yi daidai da umarnin gwamnatin jihar na tabbatar da cewa ba za a zabi wani mai shan kwaya a cikin wani ofishin gwamnati ba.
Abdul yace zuwa yanzu mun tantance sama da‘ yan takara 250 duka kan kujerar Shugaban karamar hukuma da mataimakin shugaban karamar hukuma da kuma kansiloli.
Mun gano wasu daga cikinsu da alamun shan kwaya, ba za mu fada muku sunayensu ko kananan hukumominsu ba.
Daga karshe ya yi kira ga mazauna jihar da su ci gaba da bai wa rundunar goyon baya da ake bukata don rage shan miyagun kwayoyi zuwa matakin mafi kankanta.


