Labarai
Da dumi’dumi: Babbar Kotun Tarayya tace a watan satumba za’a yanke hukunci kan shari’ar Bidiyon karbar Dollar na Ganduje.


Wata babbar kotun tarayya da ke jihar Kano ta sanya ranar 22 ga watan Satumba domin yanke hukunci kan karar da tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya shigar, na dakatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano daga bincikensa.
Lauyan hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Femi Falana, SAN, a ranar Talata, ya bayar da hujjar cewa karewar da Kotun tayi wa tsohon gwamnan ya kare ne a ranar 29 ga watan Mayu, kuma babu wata kotu a kasar da za ta ba shi kariya, ko iyalansa, ko yan majalisarsa
Sai dai lauyan Ganduje, a martaninsa, ya dage kan cewa ba a bin tsarin da ya dace, wanda hakan ke keta hakkinsa na dan Adam.


