Ƴan Ta’adda Sun Hanamu Zuwa Gonakin Mu, Inji Abbas Abdullahi (Sarki Baƙin Iyatawa)

Matsalar Tsaro Na Cigaba Da Ta’azzara A Jihar Kaduna.
Ƴan Ta’adda na cigaba da ayyukan su a yankin Giwa Muna kira da Gwamnatin Tarayya,da Jihar Kaduna, da Ƙanan hukumomin mu dasu taimaka su kawo mana agaji.
Ƴan Ta’adda nacin karen su Babu babbaka.
Yace Ƴan Ta’adda nama mana kisan gilla, su rabamu da dukiyoyin mu Su Lalata mana muhallin mu, su sace Al’umma don neman kuɗin fansa, Uwa Uba su kwashe Mata don suyi Fasadi dasu.
Wannan abin ban tsoro ne da taici. Bama iya barci a yankunan mu sabida fargaba.
Muna roƙon Don Allah gwamnati ta tashi tsaye ta kawo mana agaji. Yankin Giwa ta Yamna abin yafi ta’azzara kwakwata babu jami’an tsaro a gurin. A Kaɗage ne kawai akwai jami’an tsaro a Giwa ta Yamma kuma suna gefe ne kuma basa bawa Al’ummar yan kin mu wata agaji idan Ƴan Ta’adda sun kawo masu hari.
Babban tashin hankalin da muke ciki shine Noma ya gagare mu, kuma har ta kai ga Ƴan Ta’adda suna shigo da dabbobin sata kasuwanin mu koda kaga abinka baka isa kayi magana ba sabida mugun sharrin su.
Yankuna da abin yafi shafa.
A Giwa
-Bakali
-Tunburku
-Galadimawa
-Sabon Layi
-Basurfe
-Kawon Kaɗage
-Murai
-Ƴar mangwaro Kidandan
-Tashan zomo
-Sabon layi
Sai Yankin Ƙaramar Hukamar Igabi Da Birnin Gwari sabida munada iyakoki dasu Inda Ƴan Ta’addan suke yawo a ko ina a cikin dazuka da garurun mu.
Sarkin Baƙin Iyatawa ya ƙara da cewa Gwamnati ta kawo mana ɗauki sabida munada kayan Gona a Gonakin mu wadda dole mun bar su. Sabida irin kissa ko sacemu da barayi keyi, Gwambati don Allah ta taimaka ta kawo mana Agaji.
Muna Addu’a Allah bada ikon taimakawa ya kawo ƙarshen wannnan matsalar Inji Sarkin Baƙin Iyatawa.
Jihar Kaduna dai tana fama da matsaloli Tsaro a ciki Harda rikicin ƙabilanci a Kudancin Kaduna inda aka rasa rayuka da dukiyoyi.
