Rahotanni

A Enugu Fasto ya dirkawa almajiransa ‘yan Mata 20 Ciki Kuma Yace wahayi ne Daga Allah.

Wani Fasto dan shekaru 53 ya dirkawa mabiyansa 20 ciki inda ya bayyana cewa wahayi aka masa yayi hakan.

Yanzu haka dai faston na can tsare a wajan ‘yansanda a jihar Enugu.

Sunan Faston Timothy Ngwu wanda ke jagorantar Cocin Vineyards dake Enugu. Kakakin ‘yansandan jihar, Ebere Amariazu ya bayyana cewa an kai Faston kotu inda aka tuhumesa da cin zarafi.
Matarsa ce da abin ya isheta ta je ta gayawa hukuma. Saidai faston yace babu wadda ya tursasawa, kowacce sai da mijinta ya yadda sannan ya dirka mata cikin. Rahotan hutu dole..

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button