Akwai yiwuwar kungiyar boko haram ta tsananta kai hare hare saboda ta nunawa sababbin hafsoshin tsaron Najeriya cewa tana shirye da zuwan su, in ji Gwamna Zullum.
Akwai yiwuwar kungiyar boko haram ta tsananta kai hare hare saboda ta nunawa sababbin hafsoshin tsaron Najeriya cewa tana shirye da zuwan su.
Akwai yiwuwar kungiyar boko haram ta tsananta kai hare hare saboda ta nunawa sababbin hafsoshin tsaron Najeriya cewa tana shirye da zuwan su, gwamnan Borno Farfesa Babagana Umar Zulum ya gayawa sababbin hafsoshin tsaron Najeriya.
Gwamnan Borno Farfesa Babagana Umar Zulum ya sanar da sababbin hafsoshin tsaron Najeriya ta wayar salula cewa ya san dabi’ar ko wadanne ‘yan ta’aada ne nuna barazana ga jami’an tsaro yayin da akace an samu wani canji.
Farfesa Babagana Umar Zulum ya kara da cewa yana shawartar sababbin hafsoshin tsaron Najeriya da kada suyi wani la’akari da duk wata barazana da ‘yan ta’addan za suyi musu da zimmar sanyaya musu kwarin gwuiwa.
Farfesa Babagana Umar Zulum ya ce yana kira ga sababbin hafsoshin tsaron Najeriya da su tabbatar sun tunkari duk wasu ‘yan ta’addan kasar nan bisa sabon tsarin yaki da ta’addancin da suka samar, kuma ba tare da sun rinka sanar da dabarun ba kamar yadda aka rika samu abaya.
Zulum ya kara da cewa duk wani sabon salon yaki da ta’adda da sababbin hafsoshin tsaron Najeriya suka tanadar a yanzu to su rika boye abinsu isu isu ba tare da sun shelantawa duniya kowa ya ji ba .
Daga Kabiru Ado Muhd