An bukaci Shugaba Bola Tinubu ya nisanta Gwamnatinsa da Ganduje domin kare martabar Nageriya.

An yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya nesanta gwamnatinsa daga bai wa tsohon gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano duk wani mukami saboda faifan bidiyon cin hancin Dala da ake zarginsa da shi domin ceto martabar kasar nan a duniya.
Shugaban kungiyar masu yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya Kabiru Dakata ne ya yi wannan kiran a taron manema labarai da aka gudanar a Kano ranar Lahadi.
Har ila yau kungiyar ta yi kira ga hukumar ‘yan sanda ta kasa da kasa (InterPol) da hukumar shige da fice da kuma jami’an tsaron Najeriya da abin ya shafa da su tabbatar sun sanya wa tsohon gwamnan ido don hana shi tserewa daga Najeriya.
“Muna kira ga tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya mutunta dokokin kasa da suka hada da dokar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, sannan ya mika kansa domin gudanar da bincike domin a ba da dama ga adalci.
Wannan dabarar jinkirin da yake amfani da ita za ta nuna cewa a fakaice ya amince da zargin amma ba ya son a bincikar shi.
“Muna kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kada ya bari duk wanda ke da zargin cin hanci da rashawa ya yi amfani da hoton sabuwar gwamnatin sa a matsayin maboya domin yin zagon kasa a bincike da gurfanar da shi a gaban kotu.
“Bugu da ƙari, muna kira ga maigirma shugaban ƙasa da ya nisanta majalisarsa daga mutane irin su Ganduje don kada ƙasashen duniya su yiwa Najeriya laƙabi da cin hanci da rashawa.
Muna kira ga hukumar ‘yan sanda ta kasa da kasa (Interpol) da hukumar shige da fice ta kasa da ma sauran hukumomin da abin ya shafa da su sanya wa tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ido sosai domin kada ya gudu daga kasar kafin a gudanar da bincike”. Jagoran Convener ya bayyana.
Tun da farko a nasa jawabin, Convener ya bayyana cewa maganar cin hancin Dala ta kasance tun shekarar 2018 amma ba a ga rana ba saboda rigar da tsohon gwamnan ke da shi. A kwanakin baya ne dai hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta PICACC reshen jihar Kano karkashin Muhyi Magaji Rimingado ta sake bude shari’ar tare da gayyaci Ganduje domin gudanar da bincike.