Tsaro
An Kuɓutar da Jami’an ‘Road Safety’ Da Aka Sace A Jihar Nasarawa.
Hukumomin ’yan sanda a jihar Nasarawa sun ce an kubutar da ragowar jami’an nan na hukumar kiyaye hadura ta kasa, wato ( federal Road Safety Commission) da wasu ’yan bindiga suka sace a jihar Nasarawa.
Jami’an hukumar kiyaye haduran suna kan hanyarsu ce ta zuwa wani kwas a jihar Enugu, lokacin da lamarin ya auku a ranar Litinin ta makon jiya.
Inda daya daga cikinsu ya rasa ransa wasu shida kuma suka tsira da munanan raunuka, aka yi awon gaba da guda goma.
Daga Amir sufi

