Labarai
Ba zamu Bawa Jihar Zamfara tallafin korona ba
Daga Ibrahim Dau mutuwa Dole
Ma’aikatar Agaji da Ci Gaban Al’umma ta Najeriya ƙarƙashin jagorancin Minista Sadiya Umar Farouk ta dakatar da shirin bayar da tallafin kuɗi ga marasa ƙarfi da ta tsara yi a ƙarshen makon nan saboda matsalar tsaro.
Ma’aikatar ta bayyana haka ne yau Litinin a wata sanarwa a shafukanta na zumunta. Ta ce dakatarwar ta shafi shirin raba tallafin taki da kuma kayan abinci domin rage raɗaɗin annobar korona.
“Za a shaida wa waɗanda za su ci gajiyar tallafin lokacin da za a raba nan gaba,” in ji sanarwar.


