Tsaro

Babu Inda za a sami zaman Lafiya a kasarnan, Inji Gwamna Ortom

Gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom a ranar Alhamis, ya mayar da martani game da sace ‘yan makaranta daga jihar Katsina, yana mai cewa hakan na nufin babu inda za a samu lafiya a kasarnan.

Gwamnan ya ce lamarin da ya faru a Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati da ke Karamar Hukumar Kankara, ya bayyana cewa babu inda za a sami lafiya a kasarnan.

A makon da ya gabata ne Boko Haram suks sace wasu daliban makarantar sakandaren Kimiyya ta Gwamnati da ke Kankara, Jihar Katsina.

Kungiyar Boko Haram a wani faifan bidiyo da ta fitar ta yi ikirarin cewa an sace daliban ne don karfafa addinin Musulunci da kuma hana karatun kasashen yamma.

Gov Ortom ya yi Allah wadai da sace daliban a Katsina.

Ya bayyana hakan ne yayin ziyarar sa zuwa Babban Jami’in Kula da Tsaro, MSCC, da ke Makurdi.

A cewarsa, “Idan za a iya sace ɗaruruwan ɗalibai a cikin Katsina, mahaifar Shugaba Buhari, to, babu wani wuri da za a sake ɗaukar lafiya”.

Bugu da kari, ya bukaci Shugaba Buhari da shugabannin tsaro da su bi sabbin hanyoyin magance rashin tsaro.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button