Cibiyar CPI ta bukaci Gwamnati da ta tsaurara tsaro a kafofin yada labarai a Najeriya.
Cibiyar yan Jaridu ta Duniya ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta tabbatar da tsaro a gidajen yada labarai da Yan Jaridu sakamakon hare haren da aka kai kan kafofin yada labarai guda 5 a birnin Lagos dake kudancin kasar.
.
Shugaban kwamitin Cibiyar dake Najeriya Kabir Yusuf yayi mummunar suka kan harin da kuma lalata kadarorin kafofin yada labaran da akayi sakamakon zanga zangar da ta rikide ta zama tarzoma.
Kafofin yada labaran da abin ya shafa sun hada da Jaridar The Nation da tashar talabijin ta Televison Continental da gidajen rediyon Radio Lagos da Eko FM da Traffic FM wadanda aka cinnawa wuta.
Yusuf yace sun amince da yancin gudanar da zanga zanga da bukatar neman kadi amma kuma hari kan kafofin yada labarai abin tada hankali ne da ba zasu amince da shi ba.


