Labarai

Da dumi-dumi: Gwamna Abba Kabir ya mayar da Barr. Muhuyi Magaji matsayinsa Shugaban Hukumar Yaki da rashawa.

Gwamnan jihar Kano Engr Alh. Abba Kabir Yusuf, Gwamnan Jihar Kano, ya amince da mayar da Barr. Muhyi Magaji Rimin Gado a matsayin Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa, PCACC, domin kammala wa’adinsa.

Kuna iya tunawa cewa gwamnatin da ta shude ta dakatar da Barr Muhyi daga mukaminsa bisa wasu dalilai.

Maido dashi aikin yana tare da sakamako na nan take bisa bin umarnin kotu Sanusi Bature Dawakin Tofa
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kano ne ya sanar da wannan batu

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button